Labarai Nishadi

Kotu ta bayar da belin Naziru Sarkin Waka, ta gindaya masa sharuda

Wata kotu a jihar Kano ta bayar da belin Naziru Ahmad, Sarkin Wakar Sarkin Kano a zamanta na ranar Alhamis.

Hakan na zuwa ne bayan da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta mika mawakin zuwa kotu bisa zargin fitar da wasu wakoki ba tare da sahalewar hukumar ba.

DABO FM ta rawaito daga gidan rediyon Freedom na jihar Kano cewa;

“A zaman kotun na yau an bada belinsa akan sharadin ya kawo mutane biyu da zasu tsaya masa, daya daga cikinsu dole ya zama mai unguwa mai matakin albashi na 12 kuma dole sai ya ajiye Fasfo dinsa a kotu.”

Tin dai a jiya Laraba, jami’an tsaro suka je gidan Naziru Sarkin Waka, suka tafi dashi ofishinsu bisa tuhumar karya dokar hukumar tace fina-finai ta jihar Kano.

Sai dai ana yiwa kamun kallon nasaba da rashin goyon bayan gwamnatin jihar Kano da mawakin baiyi ba a zaben daya gabata.

Mawaki Sadik Zazzabi, Darakta Sunusi Oscar duk sun fuskanci irin kamun da akayiwa Naziru wanda duk ya bayyana sun barranta daga tafiyar gwamnatin Kano a lokacin zaben gwamna.

Karin Labarai

UA-131299779-2