Ra'ayoyi

Alakar dan Majalissar tarayya na Fagge da Al’ummar da yake wakilta, Daga Umar Aliyu Fagge

Idan aka ce wakilin al’umma ana nufin wani mutum tilo da aka zaba ya wakilci al’ummar da ya fito daga cikin su domin kare musu hakkin su ta fuskoki daban-daban, misali tun daga fuskar haskar ilimi, tsaro, sana’oi da dukkan abubuwan da zasu bunkasa rayuwar al’ummar nan.

Idan muka yi la’akari da wannan ma’anar ta wakilci zamu ga cewa wakilin alumma bawan alumma ne ba maigidan su ba.

A siyasar karamar hukumar Fagge, alaka tsakanin al’ummar wannan karamar hukuma da wanda yake wakiltar su, alaka ce da zamu iya kiranta alakar bayi da wakilin su, domin babu wata kulawa ta musamman da wannan wakilin yake bawa al’ummar karamar hukumar ta Fagge.

Hakan ya samo asali ne sakamakon kawar da kai da rashin bibiyar yadda ake tafiyar da wakilcin wannan karamar hukumar da su al’ummar karamar hukumar suka yi, dole alummar wannan karamar hukumar ta samar da wani tsari wanda zai saka ido tare da bibiyar yadda wannan wakili yake wakiltar alummar sa idan akwai inda yake bukatar gyara sai agyara masa ko a hakaitar dashi cewa ga abin da yake fa damun alumma.

Bincike ya mana nuni da cewa; Nuna halin ko in kula da mafiya yawa daga cikin masu ilimin wannan karamar hukuma shi ya bawa wannan dan majalisa damar yin wakilcin ganin dama domin babu wanda zai iya fada masa cewa Kwamaret abin da kake ba shi al’umma suke so ba ko kuma su bugi kirji su ce wakilcin ka bai yi dai-dai da bukatar al’ummar mu ba.

Duk wanda ya aminta su zama yaran sa to basu da tunanin kawowa al’umma cigaba hasalima sune ake kira ‘yan Kwamatin Koli (Main committee) kuma wannan wakilin duk yafi su ilimi da tunani don haka babu wanda zai iya gano kuskuren wannan wakili ballanata yace a gyara, kuma dukkan su bukatar kai ce ta kai su gurin shi ba wai su ringa kwabar shi ba a duk inda ya sauka daga layi.

Wannan mummunar ko ince kwadaitacciyar alaka tsakanin wakilin wannan alumma da yaran sa wanda ake wa lakabi da ‘Yan Kwamatin Koli (Main Committee} ita ce ta bawa wannan wakili damar wulakanta tare da kaskantar da al’ummar da yake wakilta, domin a gurin sa irin tunanin su sauran al’ummar da yake wakilta suke da shi.

Ina ga lokaci yayi da wannan al’umma ta karamar hukumar Fagge zata yaki wannan tsari na awon igiya inda wakilin al’umma yake amfani da wasu yan tsirari gurin auna fahimtar dubban mutane masu tunani da ilimi, ya kamata wanarabul ya gane cewa idan wadancan kwadayayyu ne sauran al’ummar karamar hukumar ba haka suke ba.

Idan an ajiye ‘Yan Kwamatin Koli a matsayin mabarata, sauran alummar kuma hakkin su suke nema domin ba alfarma wanarabul zai mana ba. 

Ya kamata Com. Goro ya sani cewa wakilin al’umma, bawan alumma ne kada kwadayin wasu ya jawa sauran al’umma raini da kaskanci a idon ka.

Idan ‘Yan Kwamatin Koli sun iya jure wulakanci da kaskanci, to bana tunanin daukacin al’ummar karamar hukumar Fagge zasu juri wannan kasassabar!


Rattabawa

Umar Aliyu Musa

05/9/2019

10:20 am

Masu Alaka

Shugabanci ne matsalar Najeriya da Arewa, Daga Umar Aliyu Fagge

Dabo Online

#Xenophobia: Abin kunya ne shugaba Buhari ya ziyarci kasar Afirika ta Kudu – Usman Kabara

Dabo Online

Ko dai a dawowa da Sultan alfarmarsa, ko ya zare hannunsa a komai, Daga Hassan Ringim

..

#JusticeForKano9: Shirun ‘Yan Arewa da Malaman ‘Social Media’ akan mayarda Yaran Kano 9 Arna

Dabo Online

‘Idan Malamai na Allah basu farga ba, shedanun malamai za su cefanar da Musulunci’

Dabo Online

Su Waye ke bautar da Matasa a manhajar Facebook?

Idris Abdulaziz Sani
UA-131299779-2