Fadan Kwankwasiyya da Gandujiyya ya fito da ‘Sabon Salo’, kashi na 2

Siyasar jihar Kano tana cigaba da yin zafi har bayan kammala zaben gwamnan jihar na shekarar 2019.

A dai dai lokacin da tsagin Kwankwasiyya suke ganin sune halastattun wadanda suka lashe zabe a jihar Kano, gwamnantin jihar ta dauki mataki irin na gallazawa abokan hamayyarta.

A halin yanzu, jihar Kano, an shiga wani kangi na kame-kamen abokan hamayya wanda ake danganta hakan da cewa; “Wanda yabi tafiyar Gwamna ya tsira.”

DABO FM ta binciko cewa; daga lokacin zaben gwamnan jihar a watan Maris, an tsare adadin ‘yan tsagin Kwankwasiyya sama da 5.

Idan baku manta ba, a makonnin da suka gabata ne dai aka aike da darakta a Kannywood, Sunusi Oscar, zuwa gidan maza. Kamun da ake kallon ya saba ka’ida duba da tuhumar da akayi masa na dora bidiyo a manhajar Youtube ba bisa ka’ida ba. Abinda masana suka ce Hukumar Tace Fina-Finai ba tada hurumi.

Masu Alaƙa  Sanarwa game da saukar Daliban Kwankwasiyya 370 a kasar Indiya

Akwai mata da mawaka wadanda sukayi irin tasu sukar siyasa a cikin wakensu, wanda suma ba’arsu ba, don yanzu haka ana kanyi musu dauki dai dai.

A ranar Laraba, 11 ga watan Satumba, jami’an tsaro suka kaiwa Sarkin wakar Sarkin Kano, Naziru M. Ahmad, goron shiga dambarwar tsagin gidajen siyarsar Kano ta hanyar daka masa wawa tare da tafiya dashi zuwa ofishinsu.

Rahotanni sun bayyana shima dai ana tuhumarshi ne a karkashin hukumar tace fina-finai wacce tace yayi waka da kalaman batanci.

Mawaki Alan Waka, shima, ya karbi nashi goron, sai dai goron Aminu Ladan Ala, mai saukin taunuwa ne, inda jami’an suka kyaleshi ya dawo gida salun alin bayan da suka kirashi amsa tambayoyi a Ofishinsu.

Masu Alaƙa  Jami’ai sunyi kame ‘Dan gwagwarmayar Kwankwasiyya’, Abu Hanifa Dadiyata

Idan baku manta ba, tin kafin alakar tayi tsamari, mawaki Sadik Zazzabi ya amsa kiran dambarwar bayan fitowar wakarshi mai taken “Maza Bayanka.”

Dambaruwar dai bata tsaya kan mawaka da fitattun jaruman Kannywood ba, ta hada har da matasan yan siyasa da ‘yan gwagwarmaya.

Matasa irinsu Mustapha Jarfa, Salisu Yahaya Hotoro da wadansu mata guda biyu, sun fantsama tsundun cikin cakwakiyar.

Duk dai a dambarwar, har yanzu ba’a san a ina matashi Abubakar Idris Dadiyata, yake ba duk da cewa daga cikin jagororin jami’iyyar APC, Alhaji Buba Galadima, yace “wani gwamna ne a Arewa yasa a kamashi.”

Sai dai hukumar DSS ake zargi dayin awon gaba da matashi wanda yayi kauron suna wajen caccaka da adawa da gwamnatin APC a Kano da Najeriya baki daya, tace ba tada hurumin ko hannu game da batan matashin ba.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.