Labarai

Kotu ta daure mawaki shekara 1 bisa wakar sukar Ganduje da yabon Sarki Sunusi

Wata babbar kotu dake da zama a jihar Kano ta daure wani matashin mawaki har tsawon shekara 1 a gidan kaso biyo bayan wakar sukar Ganduje da yayi.

Mawaki Yusuf wanda aka fi sani da AGY, ya rere wakar ne domin nuna goyon bayanshi ga Sarkin Kano Muhammadu II akan rikicin dake tsakaninsu da Gwamnan Kano wanda ta kai ga kirkirar sabbin masarautu 4 a jihar.

Sai dai kotu ta kama mawakin da amfani da kalaman bata suna da cin mutuncin gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

‘DABO FM ta gano cewa ‘Yan sanda sun kame mawakin ne a daren Litinin tare da aike shi gaban kotu mai Lamba 72 dake Noman’s Land a birnin Kano.

Kotu ta kame AGY da laifuka 3, wanda tace ya saki wakar da bidiyo batare da sahalewar hukumar tace fina-finai da wakoki ba hadi da bata sunan Dr Abdullahi Umar Ganduje, kamar yadda DABO FM ta binciko.

Karin Labarai

Masu Alaka

Wallahi munyi aringizon ƙiri’u a Kano, – Wani Jagoran APC a Kano

Dabo Online

Kamfanin Lantarki na KEDCO ya na bin Kanawa bashin Naira biliyan 148

Dabo Online

Tarauni: Hanan Buhari zata kaddamar da koyar da mata 100 ilimin daukar hoto wanda dan majalisa ya dauki nauyi

Muhammad Isma’il Makama

Kano Municipal: APC batada ‘dan takarar majalisar tarayya – INEC

Dabo Online

Satar yara a Kano: Fiya da yara 38 yan kasa da shekaru 3 aka sace a karamar hukumar Nassarawa

Muhammad Isma’il Makama

Yanzu-Yanzu: El-Rufa’i ya bawa Sanusi II Murabus babban mukami, kwana 1 da sauke shi

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2