‘Yan Kwallon Najeriya ta mata sun samu tafiya gazaye na 16 a gasar kofin duniya

Kungiyar kwallon kafa ta mata mai wakiltar Najeriya ta “Super Falconets” ta samu damar shigewa zagaye na 16 a gasar cin kofi duniya da ake bugawa a kasar Faransa.

Duk dai Najeriya tayi rashin nasara a karawarta ta kasar Faransa, sabuwar dokar FIFA ta bawa kasar damar fitowa a matsayin zakarun masu rashin nasara masu kwazo da da’a.

Kasar Najeriya da Kamaru ne suka samu wannan tagomashin daga nahiyar Afrika kuma suna kawai kasashen da suka garzaya zagaye na 16.

Kamaru ta samu damar fitowa bayan da ta doke kasar New Zealand daci 2-1 a cikin rukunin E.

Najeriya ta samu shiga zagayen 16 ne bayan da kasar Chile ta doke Thailand 2-0 a wasan karshe na rukunin F.

Masu Alaƙa  Kociyan Najeriya Stephen Keshi ya cika shekaru 3 da mutuwa

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: