Labarai

Kotu ta yanke wa mutumin da ka kama da laifin kisan takwaran ‘Dangote’

Wata babbar kotun Kano da ke zama a hanyar Miller ta yanke wa wani mutum mai suna Yakubu Dalha na kauyen Tsangaya a karamar hukumar Albasu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kotun karkasin jagorancin Jastis Yusuf Ubale Mohammed ta hukunta Yakubu kan kasancewarsa da hannu a mutuwar wani Zakariyau Bala wanda aka fi sani da Dangote.

Sashin Hausa na sashin Legit.ng ya rawaici cewar; masu kara karkashin jagorancin Abdullahi Bature, sun gabatar da shaidu bakwai wadanda suka bayar da hujja kan mutumin da aka hukunta.

Yakubu ya shiga cacar baki da Dangote kan lamuran siyasa; a halin haka sai wanda aka hukuntan ya dauki icce ya rafka wa marigayin wanda hakan ya sanya shi samun raunuka a kai da kafadarsa.

Sajen Tijjani Sule wanda ke aiki da rundunar yan sandan reshen Albasu a nashi shaidar ya bayyana ma kotu cewa ya yi bincike a kan lamarin, cewa an kama mai laifin sannan an samu wani jawabi daga Yakubu wanda ke fallasa laifinsa.

Wani likita, Dr Abdulkareem Sule, da ke aiki a asibitin kwararru na Murtala Muhammad ya bayyana cewa Dangote ya isa asibitin matacce.

Lauyan mai kara ya sanar da kotu cewa lamarin ya afku ne a ranar 22 ga watan Agusta, 2012 a kauyen Tsangaya, inda ya kara da cewa lokacin da marigayin ya ji rauni, makwabta da yan uwa sun dibe shi zuwa wani asibtin kudi a Dutswe, jahar Jigawa.

Asibitin Dutse suka mayar dashi zuwa asibitin koyarwa na Aminu Kano inda daga nan aka kais hi asibitin Murtala inda aka tabbatar da mutuwarsa. Wanda ake karar, wanda ya yi watsi da shaidun da aka bayar a kansa, ya kira shaidu hudu domin su karyata tuhumar da ake masa.

UA-131299779-2