Home LabaraiAn daga auren Sulaiman da baturiyar Amurka ‘sai baba ta gani’

An daga auren Sulaiman da baturiyar Amurka ‘sai baba ta gani’

by Dabo Online
0 comments

Auren matashin nan dan jihar Kano, Sulaiman Isa da baturiyar Amurka, Jeanine Sanchez, ya samu tangarda bayan da aka dagashi babu ranar yi.

Hakan na zuwa ne bayan da kasar Amurka ta dakatar da baiwa ‘yan Najeriya da izinin shiga ‘Visa’ ta masu neman mafaka da ma’aurata.

DABO FM ta tattara cewar a watan Janairu ne aka tsayar da watan Maris a matsayin watan da masoyan biyu zasuyi aure bayan ita baturiyar ta kamalla tanadar takardu domin daurin aure.

Da yake shaidawa Daily Trust, mahaifin Sulaiman, ya bayyana cewar da zarar an sanya sabon lokacin, zai fadawa manema labarai.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00