/

Kotun koli ta tabbatar ‘Abba Gida Gida’ a matsayin wanda ya lashe zaben PDP a Kano

Karatun minti 1

Babbar kotun kolin Najeriya ‘Supreme Court’ ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin sahihin dan takarar gwamna a jami’iyyar PDP na jihar Kano bayan da Ibrahim Little ya shigar ta karar kalubalantar zaben.

Kotun kolin ta kori kara tare da sake jadda hukuncin da wata kotu tayi a jihar Kano na tabbatar da sahihancin Abba Yusuf na zama wanda yake takarar gwamnan a jami’iyyar ta PDP.

DABO FM ta gano cewa a ranar 18 ga watan Afirilu wata kotun daukaka kara dake KAduna ta kara tabbatar da Abba K Yusuf a matsayin sahihin dan takarar PDP bayan da wata Kotun tarayyar ta ruguje zaben.

Da yake bayyana hukuncin, mai shari’a Tanko Hussaini yace kotun tarayyar ta yanke hukunci batare da la’akari da cewa wanda ya shigar da karar, Ibrahim Little, bai fafata a zaben da yake kalubalanta ba.

Daily Nigerian ta rawaito cewa a ranar 4 ga watan Mayu, Kotun tarayya dake da zama a jihar Kano ta kori Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar gwamnan Kano a karkashin jami’iyyar PDP bayan da mai shari’a Lewis Allagoa yace jami’iyyar PDP bata gudanar da zaben fidda gwani a Kano ba.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog