Kudi da mukami daga Iran ne suka ja Al-Zakzaky zuwa Shia – Yayan Zakzaky

Sheikh Muhammad Yakubu shi ne yayan shugaban IMN ta Shi’a, Sheikh Ibrahim Al-Zakzaky.

Sheikh Muhammad Yakubu ya bayyana yacce kasar Iran ta janye ra’ayin Zakzaky zuwa fadawa tafiyar Shi’a bisa dalilin kudaden da suka rika bashi.

Yayan Al-Zakzaky ya bayyana haka ne a yayin wata ganawarshi da wakilin Jaridar PUNCH a filin tashi da saukar jirage na Mallam Aminu Kano dake jihar ta Kano a kokarin shirin da yake na tafiya kasar Saudiyya.

Sheikh Muhammad da yake amsa tambayar, “Gashi kai ‘yayan Zakzaky ne, wane irin mutum ne lokacin da yake karami?”

“Mun yi samartakarmu tare da ‘dan uwa na Al Zakzaky. Mutum ne mai fasaha, basira hadi da baiwar kwakwalwa mai hadda. Mutum ne shi kamar na’urar nadar sauti, duk abinda ya karanta take zai haddace kuma yayi bayanshi dalla-dalla. Tare mukayi karatun Firamare, nan ta tabbata yana da basira.”

Duk da cewa ku ‘yan uwan juna ne, Gashi shi yana Shi’a, kai kuma kana Sunni, meyasa haka? Daga wana lokaci aka samu wannan chanjin?

“Bayan mun kammala karatunmu na Firamare, Al-Zakzaky ya samu gurbin karatu makaranta ‘Advanced Teachers College Kano’, ni kuma na tafi ‘Advanced Teacher’s College Katsina’.

“Daga nan ne ya fara yin magana da kasar Iran. Al-Zakzaky ba ‘dan Shi’a bane a wannan lokacin. Amma bayan ya kammala karatun Digirinshi a jami’ar ABU Zaria, daga nan ya fara hada dalibai don yaduwar Musulunci kamar Malami.

“Ya samu wannan tunanin ne daga kasar Iran, daga baya ya fara samun kudi. Iran suka gayyace shi zuwa chan kasar domin ya shiga Shi’a, daga nan suke daukar nauyinshi da kudin.

Asalin Al-Zakzaky dan Sunni ne, kasar Iran ce suke janyeshi da kyauta zuwa Shi’a.

“Ya (Zakzaky) ya zama dan SHi’a bayan zuwanshi kasar Iran, biyo bayan alkawura da suka yi masa ciki harda nada shi babban jakandan Shi’a a Najeriya. Ya chanza ne saboda kudaden da Iran take daukar nauyinshi da su.”

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.