Dan Fansho ya mayarwa gwamnatin jihar Bauchi rarar miliyan 1 daga kudaden da aka biyashi

Shugaban kungiyar ma’aikata ‘yan Fansho na jihar Bauchi, Habu Gar, ya shawarci gwamnatin jihar da ta kula sosai wajen biyan kudin ‘yan fansho da takeyi.

Habu ya bayyana cewa a tsarin biyan kudi da gwamnatin take yi a yanzu, kowanne ma’aikaci ana kara masa kaso 500 daga abinda ya kamata a bashi.

DABO FM ta rawaito cewa; Shugaban kungiyar ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa, an baiwa ‘dan fanshon ‘Cheque’ na Naira miliyan 1.2 maimakon N200,000 da take hakkinsa.

“Ranar Talata, naje wajen da ake biyan kudin ‘yan fanshon, ya gano cewa an baiwa wani miliyan 1 a maimakon Naira 200,000.”

“Lokacin da ‘dan fanshon banki, aka bashi miliyan 1.2, sai dai ya dawo da Naira miliyan dayar data karu akan kudin nashi.”

Ya kara da cewa mutumin yana bin gwamnatin Naira miliyan 1.2 na ‘Gratuity’, amma an bashi miliyan daya a lokacin da tsohon gwamnan Muhammad Abubakar ya cire Naira biliyan 2 domin rage bashin da ‘yan fanshon suke bi.

Daga karshe ya bayyana cewa zasuyi bincike domin gano musabbabin yin kuskeren.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.