Labarai

Kudin da ake biya na wutar Lantarki zai karu daga shekarar 2020

Masu amfani da wutar Lantarki a Najeriya zasu biya kimanin Naira tiriliyan daya da rabi a shekara mai kamawa.

Hakan na zuwa ne bayan amincewa da kara fashin Lantarki da gwamnatin tarayya tayi, kamar yacce Jaridar PUNCH ta rawaito

Binciken da Jaridar ta gabatar ya bayyana cewa; an samu karin biliyan 600 daga cikin biliyan 900 da aka kiyasta cewa kamfanunuwan lantarkin Najeriya zasu samu.

Jaridar tace wakilinta ya binciko cew daga shekara mai kamawa, za’a samu karin N8 zuwa N14 a duk KiloWatt din da aka sha a awa 1.

Dabo FM ta rawaito cewa duk dai a shekerar 2020, kamfanunuwan rarraba hasken lantarki 11 da suke Najeriya, zasu samu karin adadin yawan wutar Lantarki da suka saba samu.

Comment here