Ra'ayoyiTaskar Matasa

Meyasa wasu mutane suke jin tsoron tofa albarkcin bakinsu wajen kawo gyara a siyasa?, Daga Umar Aliyu Musa

Wannan ita ce babbar tambayar da take ci min tuwo a kwarya kuma kullum nake ganin baikon wannan alummar da suke jin tsoron kawo gayra a siyasar mu ta wannan zamani na wa kaci-wa tashi, saboda wani rarraunan uzirin su kamar haka:-

A duk inda aka ce siyasa ana nufin wani fage ne da wakilan alumma suke nuna bajintar su, idan wani ya gaza sai wani ya gwada.

A nasu bangaren alummar da ake mulka suna da halartacciyar dama da kundin tsarin mulki ya basu gurin fadin albarkacin bakin su wanda hakan zai saka wa wannan wakilan kaimi gurin sauke nauyin da aka dora masu a matakin gwamnati daban-daban.

Kunga kenan yin magana akan a gyara can da can ba tare da cin mutuncin wani dan siyasa ba halak ne a tsarin wannan siyasar tamu kuma ya cancanta ayi hakan.

Binciken da nayi ya min nuna da cewa mutane masu mutunci suna jin tsoron tsoma bakin su ne a siyasa saboda gudun kar wani jahilin ko wawa yayi musu jahilci a lokacin da suka kawo wani tsokaci dangane da wakilin su ko gwamnan su, hakan ya samo asali ne sakamakon daurewa siyasar bara da jagaliyanci gindi da wasu daga cikin wakilan alumma suka yi ne.

Sai kaga mutum akili mai hankali yayi rubutun basira cike da ilimi akan wani dan siyasa kwatsam sai wani ya maida martani da zagi ko cin mutuncin masu mutunci, alhalin bai san cewa duniya yake nunawa waye shi ba.

Ba lefi bane idan yin hakan ya zama dole, amma gaskiya a tunanina bai kamata jin tsoron wani wanda bai san abinda yake ba ya hana mutane masu tunanin da ilimi yin magana akan siyasa ba.

Domin rashin yin cakulkuli ga wadancan yan siyasar shi yake basu damar danne hakkin alumma ba tare da wata fargabar cewa wasu masana ko daliban ilimi zasu yi musu gyara kayanka ba.

Ina ga ya zama wajibi a wannan gabar duk wanda yake ganin yana da wata gudunmawa dangane da yadda ake tafiyar da tsarin shugabanci ko zai a karamar hukumar sa ya tashi gurin bada irin gudunmawar sa.

Wannan nauyin bai rataya a wuyan wani mutum daya ba, malaman jami’a da takwarorin su na kwalejojin ilimi da iyayen kasa duk suna da rawar takawa gurin samar da ingantaccen shugabanci/wakilci a kowace alkarya, mu da muke dan yin kokari muna yin iyaka namu ne kuma abin da wadannan mutanen {farfesoshi da daktoci da masu unguwani} suka hango bai zama lallai mu hango shi ba tunda har yanzu tatata muke yi a fagen neman yancin alumma.

Lokaci ya wuce da jin tsoron jahilcin jahilan yan siyasa zai hana mu fadar gaskiya akan kowane dan siyasa, a duk lokacin da wani haziki yayi nuni da a gyara ko kuma ba ayi abin da ya dace ba a can kamata yayi a duba idan akwai bukatar gyaran, idan kuma wani daga cikin wawan yan siyasa yayi kokarin zagi ko cin mutuncin ka sai ka dauki matakin da shari’a ta tanadar bayan ka nunawa duniya irin tarbiyar da iyayen sa suka bashi a rayuwa.

Kadan daga cikin abin da na nazarta a siyasar wannan zamanin kenan📖📚


Rattabawa

 Umar Aliyu Musa.

Oumaraliyu@gmail.com

24/9/19

Comment here