Labarai

Kudirin mu shi ne saita ra’ayin matasa-Kwamared Mazadu

Majalisar Matasa ta Kasa reshen Karamar Hukumar Zariya, ta gudanar da taron ganawa da masu ruwa da tsaki a sha’anin kungiyoyin da suke gundumomin Dambo da Wuciciri dake yankin Karamar Hukumar.

Da yake jawabin maraba a wurin taron, Shugaban Kungiyar, Kwamared Usman Hayatu Mazadu, ya ce, tun bayan da aka rantsar da su a watan Disambar da ta gabata, suka kudiri aniyar farfado da Kungiyar, tare da aiwatar da sabbin shirye-shiryen da zasu ciyar da kungiyoyin Karamar Hukumar Zariya a gaba.

A cewar sa, Bisa wannan tsarin ne, ya sa suka kudiri aniyar zagawa dukkanin gundumomi 13 domin gano wasu daga cikin matsalolin da Karamar Hukumar Zariya ke fuskanta, tare da ganawa da masu ruwa da tsaki domin shawo kan matsalar.

Ya kara da cewa, abun da suka gani da abun da suka amsa a rubuce, shi ne za su gabatar ga matakan gwamnati a gaba Saboda cika alkawuran da suka daukarwa ‘yan Najeriya, musamman lokacin Yakin naiman zaben shekarar dubu biyu da sha biyar da ta gabata.

A cewar Shugaban Kungiyar, Majalisar Matasa ba Majalisar siyasa ba ce. Majalisa ce da ke lalubo matsalolin matasa tare magance su.

Ya bada misalin aikin gyaran gadan dake sabuwar hanyar Jos, wanda kuma yana yankin Gundumar Dambo ne, inda ya ce, bisa koke-koke da koraf-korafe daga mutanen yankin, ya sa suka sanar da gwamnatin jihar, kuma cikin hanzari gwamnatin ta dauki haramar gyaran gadar, wanda yanzu haka yana kan gudana.
Da kuma shigar da korafi ga gwamnatin jihar Kaduna, a kan makarantar Nuhu Bamalli dake Zariya, bisa rashin wasu wadatattun kayan aikin, wanda nan ma tuni gwamnatin Jihar Kaduna ta aiwatar da kaso mai dama na bukatar da Majalisar ta gabatar mata.

Usman Hayatu Mazadu, ya kara da jadada cewa, kowwa na da gudunmuwa da zai bada domin kawo cigaba a yankin sa, a don haka ne ma ya sa koda yaushe basu kasa a gwiwa wurin fadakar da matasa hakkin da ya rataya a kansu domin cigaban su da kasa baki daya.

Tun farko da yake nashi jawabin, sakataren yada labarai na Majalisar, kwamared Umar Abubakar, ya ce, abu ne sananne kuma a fili irin kokarin da Majalisar Matasa ke yi domin magance wasu matsalolin alumma, da suka Shafi ilimi, lafiya, sana’o’i da kuma zama tsani tsakanin su da gwamnati.

A yaba ga sabbin jagororin Majalisar, domin aikin da suke ba dare ba rana domin daga martabar Majalisar da ma ayyukan ta.

Taron dai ya kawo karshe tare da gabatar da korafe-korafe daga Al’ummomi mabanbanta da suka halarci taron, Wanda ya shafi samar musu da ayyukan more rayuwa da kuma romon damokradiyya Wanda wasu yankunan tuni suka jima suna warba.

Karin Labarai

UA-131299779-2