Yi wa Mata kaciya ba Addini bane, muguwar Al’ada ce kuma cutarwa ne -Sheikh Gumi

Babban Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa; Yi wa Mata kaciya, ba addini bane.

Malamin ya kara da cewa “Cutarwa ne kuma bashi da madafa a addinin Musulunci.”

DABO FM ta binciko karatun Malamin wanda ya gabatar mai taken ‘Babin Hajji’ a ranar 21 ga watan Satumbar 2019 a jihar Kaduna.

Malamin ya sukwano karatun da ya bayyana hanin saduwa tsakanin ma’aurata a yayin gudanar da aikin Hajji.

“Malik yace; Wanda ya lalata Hajji, ya wajaba akanshi yayi hadaya.”

“Menene yake lalata Hajjin? Haduwar kaciya guda biyu, sune suke haduwa su lalata aikin Hajji, ma’ana kaciyar Namiji da Mace.”

Sai dai anan Malamin ya bayyana cewa maganar Imam Malik da ya ce Kaciya, “Kinaya ce” ma’ana ya boye sunan al’aurar mace.

Masu Alaƙa  Rikicin Zamfara: Wallahi abinda yake faruwa yafi karfin Shugaba Buhari - Sheikh Abdallah Gadon Kaya

Ya bayyana cewa; “Kaciya ga Maza, Sunnah ce, amma ga Mata kuma karramawa ce kuma wata al’adace da tuntuni Larabawa sukeyi.”

Malamin ya kawo Hadisai wadanda sukayi magana akan yiwa Mata kaciya, sai dai yace dukkanin Hadisan, da’ifai ne musamman wanda Abu Dauda ya rawaito.

Haka zalika, ya alakanta yiwa Mata kaciyar a matsayin dalilin dake sanya Mata daukar tsawon lokacin kafin biyan bukatarsu ta ‘yan Adam a cikin Aure domin shine wajen jin dadin nasu.

“Saboda haka yiwa Mata kaciya, cutarwa ne. Tana da bukata sosai kamar yacce Namiji yake da bukata, dalilin haka, al’umma bazasu haramta mata abinda Allah bai haramta mata ba.”

Masu Alaƙa  Kano: Har Bature ya gama shegantakarshi a Najeriya, bai yi abinda muke gani yanzu ba - Sheikh Dahiru Bauchi

“Ya wajaba a dena, a kuma dena alakantashi da Sunnah tinda gashi har ansamu yana cutawa.”

Karin Labarai

Leave a Reply

Your email address will not be published.