//
Thursday, April 2

Kyan Alkawari: El-Rufa’i ya sanya ‘danshi na cikinshi a makarantar Firamare ta gwamnanti

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa’i, ya sanya danshi, Abubakar, a makarantar Firamare ta gwamnati.

Hakan na zuwa ne bayan da gwamnan yayi alkawarin sanya danshi a makarantar gwamnati idan ya cika shekaru 6 tin a lokacin yakin neman zabenshi da yayi. – Daily Nigerian ta tabbatar.

Hakan wani mataki ne na samun inganci tare da nagartar karatu a makarantun jihar.

Gwamnan ya bayyana sanya dan nashi a makarantar ne a shafinshi na Twitter inda yace;

“Yau Abubakar Saddiq El-Rufa’i ya zama dalibin aji Firamare na 1 a Kaduna Capital school.”

Masu Alaƙa  EL-Rufai ya gindaya tsauraren sharuda 7 kafin amincewa da tafiyar Al-Zakzaky kasar Indiya

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020