Al'adu Labarai

Kun taba ganin yacce ake Hawan Dokin Kara? Mutanen Fagge a jihar Kano suna gayyata

Al’ummar karamar hukumar Fagge dake cikin birnin jihar Kano, sunyi shura wajen yin sana’o’in Hannu musamman wajen dinkin kaya irin na Hausawa.

Sai dai ba’a iya nan mutanen unguwar suka tsaya ba, sunyi shura wajen raya al’adun Hausawa ta hanyar yin wasanni wadanda aka faro tin Iyaye da Kakanni.

Hawan Sallah, al’ada ce ta Hausawa da akeyi domin nuna karshen azumin Ramadan, harma akanyi a lokacin Sallar Layya duk dai don murna da lokacin Idi. Sarki ne yake fitowa ya zagaye mutanen kasarshi kaana kuma ya koma gida.

Suma a nasu bangaren, Yara da Matasa sukan shirya irin nasu hawan domin farin ciki da nishadi.

Su kan kwaikwayi dukkanin irin abinda akeyi a hawan Sallah na gaske, suma suyi shi domin nishadantuwarsu da raya al’adarsu.

A karamar hukumar Fagge, an dauki Hawan Sallar Kara a matsayin babban biki wanda matasan unguwar suke shiryawa duk shekara.

Hawan Sallar Dokin Kara na shekarar 2019.

Mazauna unguwar wadanda sukayi aure, mutane da dama daga sassan jihohin Najeriya suna halartar bikin domin irin kayatarwa da bikin yakeyi a zukatan kowa.

Sai dai a shekarar da ta shude ta 2018, an zargi tsohon Dan Majalissar jiha mai wakiltar karamar hukumar Fagge, Hon Yusuf Abdullahi Ata, da kawo wa bikin cikas ta hanyar yin amfani da matsayinshi na Kakakin Majalissar Kano a wancen lokacin, inda ya turo Jami’an tsaro sukayi awon gaba da wadanda suka shirya Hawan Karar bisa wasu dalilai da aka bayyana da “Son Rai”.

A wannan karon, masu shirya taron sun bayyana shirinsu na yin gagarumin Hawan Sallar wanda sukace ba’a taba yin irinshi ba.

2018.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun, Sakatare, Ibrahim Galadima da mai hulda da Jama’a, Abubakar Ammani, na Kungiyar Raya Al’adun Gargajiya ta Matasan Fagge, tace za’a gudanar da Hawan Sallar a ranar Lahadi, 1 ga watan Satumbar, 2019.

“A madadin Sarkin Dokin Kara na Fagge, Sarki Jamilu Yakubu (Dan Yellow), yana sanarwa al’umma cewa ranar Lahadi, 1 ga watan Satumba, za’a gabatar da hawan dokin kara na Fagge in Allah ya yarda.”

Sanarwar tace za’a hadu a layin Mallam Muttaka da karfe 4 na yamma, a unguwar ta Fagge.

Karin Labarai

Masu Alaka

Shattiman Dutse ya cika shekaru 60 a kan karagar Mulki

Rilwanu A. Shehu
UA-131299779-2