Labarai

Sabuwar shekarar Musulunci: Yau 1 ga Muharram a wasu kasashe

A dai dai lokacin da watan karshe na jadawalin watannin Addinin Musulunci, Zhul Hijja ya zo karshe, kasashen Musulmai sun fara duban sabon wata.

Zuwa yanzu, kasashen Jordan da Aljeriya sun bada sanarwar ganin sabon watan Al-Muharram a daren jiya Alhamis, 29 ga watan Agustar 2019.

Hakan ya sa ranar Juma’a, 30 ga watan Agusta ya zama daya ga sabuwar shekarar Musulunci ta 1441.

Wani ma’aikaci a hukumar duban wata ta ICOP ta kasar Jordan, Inginiya Muhammad Odeh, ya bayyana cewa sun ga watan ne ta hanyar amfani da sabuwar fasahar ganin hotuna ta CCD bisa rashin ganin watan da ido da hukumar na’urar ‘Telescope’.

DABO FM ta binciko cewa; a kasar Aljeriya kuwa, Dr Yunus Zakour daga garin Batna, jami’i a hukumar ganin wata ta kasar ya bayyana cewa sun ga watan ne batare da amfani da wata na’ura ba duk da an wayi gari da hazo a garin.

Karin Labarai

UA-131299779-2