Kotu ta kwace kujerar Dan Majalissar tarayya na APC ta bawa PDP a Kano

Kotun dake sauraren korafin zaben Sanatoci da ‘yan Majalissu a jihar Kano ta kwace kujerar Majalissar tarayya ta wakilcin karamar hukumar Takai/Sumaila daga hannun Shamsudden Dambazau na APC.

Kotun ta baiwa hukumar INEC umarnin bawa dan takarar PDP, Surajo Kanawa, shaidar lashe zabe.

Idan ba’a manta ba, Kotu ce ta kwace kujerar daga hannun tsohon mai baiwa shugaba Buhari shawara akan Majalissar, Hon Kawu Sumaila bisa dalilin rashin fafatawa a zaben fidda gwani ta baiwa Shamsudden Dambazau.

Shamsudeen ne ya shigar da kara bisa cewa Kawu Sumaila bai yi zaben fidda gwani ba, hasalima ya nemi takarar tsayawa Sanatan ta Kudu ne, wanda tsohon gwamnan jihar Kano, Kabiru Gaya, ya kayar da shi.

Masu Alaƙa  Kotu tayi watsi da karar Atiku, Buhari yayi nasara a kotun zabe

Bincike da nuna cewa Jami’iyyar APC ce tayi wa Kawu Sumaila, tallar kujerar majalissar Tarayyar domin rage masa radadin kayin daya sha a hannun tsohon gwamnan.

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: