Labarai

Kungiyar Fityanul Islam ta je ziyarar ban girma ga Mai Martaba Sarkin Zazzau

Shugaban Kungiyar Fityanul Islam ta kasa reshen Jihar Kaduna, Sheikh Rabi’u Abdullahi Zariya, ya jagoranci tawaga ta musamman, domin kai gaisuwan ban girma ga mai Martaba Sarkin Zazzau kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna, Alh Shehu Idris, da bayyana masa shirye-shiryen da Kungiyar ke yi, na gudanar da gagarumin wa’azi a fadan mai Martaban nan bada jimawa ba.

Tawagar, wanda ta kumshi wasu daga cikin Shuwagabannin Jiha da na kananan hukumomin Sabon Gari da Giwa da Kudan da kuma Karamar Hukumar Zaria.

Tun farko da yake jawabi, Shugaban Kungiyar na Jiha, Sheikh Rabiu Abdullahi, ya ce, a watannin baya, Kungiyar ta gudanar da taron wa’azuzzuka wasu sassan Jihar Kaduna, bisa wannan dalilin ne, kungiya ta jiha, ta zabi Karamar Hukumar Zaria a matsayin Karamar Hukuma ta gaba da za’a gudanar da irin wa’azin.

Ya kara da cewa, wa’azin na Zaria, zai maida hankali ne kan batun zaman lafiya da inganta tsaro da kuma hadin kai.

Kuma ya shaidawa mai Martaba kokarin da suke na hadin kan Musulmin Jihar Kaduna, a saboda hakan, ya sa aka samar da wata Kungiya da take da manufar hada kan dukkanin kungiyoyin addinin musulunci a Jihar Kaduna Wanda Kuma tuni wannan shiri ya yi nisa.

Da yake maida jawabi, Mai Martaba Sarkin Zazzau Alh Shehu Idris, ta bakin mai taimaka masa a fannin sadarwa da hulda da Jama’a Alh. Abubakar Ladan, Ciroman Shantalin Zazzau, ya yaba ma kokarin da Shuwagabannin Kungiyar Fityanul Islam ke yi, tare da tabbatar masu da basu cikakken hadin kai da goyon baya a dukkanin shirye-shiryen su.

Kuma ya yi kira gare su wurin ci gaba da fadakar da al’umma na tashi a koyi ilimin zamani da na addinin domin samun tsira a nan Duniya da Gobe Alkiyama.

Karin Labarai

UA-131299779-2