Labarai

Fitaccen mai shirya bidiyo a kasar Koriya ta Kudu ya karbi Musulunci ta sanadiyyar ‘Youtube’

Anyi gyara ranar 25 ga watan Fabarairun 2020.

Fitaccen Matashin, Daud Kim, dan asalin kasar Koriya ta Kudu, ya karbi addinin Musulunci.

Bayan bibiya da samun tabbaci, DABO FM ta tabbatar da cewa jarumin ya koma addinin Musulunci ne bayan binciken bidiyoyi da karatuttukan Musulunci a kafar Youtube.

Tin dai bayan wani lokaci, jarumin ya fara yin bidiyo akan yardar cewa lallai akwai wanda ya halicci abubuwan da suke faruwa a duniya.

Bayan shafe watanni masu tsayi da fara bincike da yin bidiyo a kan musulunci, Daud Kim, ya karbi Musulunci a ranar 25 ga watan Satumbar 2019.

DABO FM ta binciko cewa ya chanza sunanshi daga Jay Kim zuwa Daud Kim bayan ya karbi Musulunci.

Zuwa yanzu da muke hada wannan rahotan, Daud Kim, yana da mabiya 713,000 a tasharshi ta Youtube mai sunan Daud Kim (Alkaluman watan Oktoba) wanda a yanzu mabiyanshi suka haura Miliyan 1 (Ranar 7 ga Disamba 2019), a yau kuma Talata, 25 ga Fabarairun 2020 yana da mabiya miliyan 1 da dubu dari 450. Yana kuma da mabiya 407,000 a Facebook, 75,600 (78200 a yau) a Instagram.

Daga ranar 25 ga watan Satumbar 2019 da jarumi Daud Kim ya karbi Musulunci, ya samu karin mabiya 195,000.

Masu Alaka

Masu ruwa da tsakin Shari’a 500 sun sanya hannu a takardar bukatar tsige Donald Trump

Hassan M. Ringim
UA-131299779-2