Home LabaraiKungiyar Fityanul Islam tayi kiran Gwamnati da ta yi Gadar Sama a Gwargwaji ta jihar Kaduna

Kungiyar Fityanul Islam tayi kiran Gwamnati da ta yi Gadar Sama a Gwargwaji ta jihar Kaduna

by Mu’azu A. Albarkawa
0 comments

Kungiyar Fityanul Islam tayu kiran gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jihar Kaduna da su duba yiwuwar yin gadar sama a Gwargwaji da ke karamar hukumar Zariya.

Wannan bukatar ta fito ne daga shugaban kungiyar Fitiyanul Islam na
Karamar hukumar Zariya, Alhaji Abdulqadir Falalu Gwargwaji, a lokacin
da ya zanta da wakilinmu da ke Zariya.

Alhaji Abdulqadir Falalu ya ci gaba da cewar, a wannan waje da ake
kira Gwargwaji, a duk rana ana rasa rayukan al’umma maza da kuma mata dare da rana, a dalilin yawan motocin da suke bin hanyar, ba tare da
tafiya a hankali daga ma su abubuwan hawa da suke amfani da wadannan
hanyoyi ba.

Da shugaban Fitiyanul Islam a karamar hukumar Zariya Alhaji Falalu
Gwargwaji, ya juya ga ma su abubuwan hawa da suke tasowa daga Kaduna da wadanda ke tasowa daga Kano da kuma wadanda ke fitowa daga tsohuwar hanyar Birnin Gwari, ya shawarce su da su rika saurarawa a duk lokacin da suka kasance a Gwargwaji, domin kawo karshen matsalolin rasa
rayukan da ake yi a duk rana.

A dai zantawa da aka yi da Alhaji Falalu, ya yi kira ga hukumomin kula
da lafiyar hanyoyi [ FEDERAL ROAD SAFETY COMMISSION ] da ta [KASTELIA], da su zauna teburi guda a tsakaninsu, domin lalubo hanyoyin da suka dace, da za su zama silar rage hadurran da ake yi a wannan waje da aka ambata.

In an yi wannan, a cewar Alhaji Abdulqadir Falalu Gwargwaji, zai kawo
qarshen matsalolin rasa rayuka da ke faruwa a Gwargwaji a duk rana,
kamar yadda aka ambata.

Da kuma ya juya ga al’umma da suke ratsa wadannan hanyoyi kuwa, sai ya
shawarce su da su rika kula da dokokin ratsa hanya a duk lokacin da
suka tashi ratsa wadannan hanyoyi da aka ambata.

A karshe ya yi kira ga kungiyoyin sufuri da suke da rassansu a Gwargwaji, da su tashi tsaye na ganin sun bayar da gudunmuwarsu, domin kawo qarshen wannan matsala na yawaitar hadurra da kuma rasa rayukan al’umma a wadannan hanyoyi.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00