//
Thursday, April 2

Kwanaki 100: An zabi Ganduje a matsayin gwamnan da yafi kowanne ‘Daraja’ a Najeriya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

An zabi gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gwamnan da yafi dukkanin gwamnonin Najeriya wajen gwazo da aiki tukuru.

Kungiyar Dimokradiyya ta Afirika dake da zama a kasar Senegal ce ta baiwa gwamnan lambar girmamawar.

Babban mataimakin gwamna jihar Kano, Abba Anwar, ne ya sanar da haka a wata takardar da ya baiwa manema labarai a ranar Lahadi.

“Awanni 24 bayan cikar kwanaki 100 da gwamnonin da aka rantsar ranar 29 ga watan Mayu sukeyi, wata kungiyar Afirika ta Yan Dimokradiyya ADAN ta zabi gwamnan Kano, Dr Abdullahi Ganduje, domin bashi lambar yabo.”

“Bayan duba ayyukan da sauran gwamnoni sukayi a cikin kwanaki 100 na fara aikinsu, kungiyar ta zabi gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin gwamnan da yafi kowanne gwamnan Najeriya na kwanaki 100 da akayi da kama aiki.”

Shugaban gudanarwar kungiyar na reshen Afirika ta Yamma, Samson Theodore, ne ya sanyawa lambar yabon hannun, inda kungiyar tace tayi duba ne a fannonin Ilimi, Lafiya, Noma, Tsaro, Tattalin arziki da ayyukan raya kasa kafin fitar da gwamna Ganduje a matsayin gwarzo.

Masu Alaƙa  Zaben Gwamna: Ganduje ya kammala kada kuri'arshi

Kungiyar ta kara da cewa; Bata zabi gwamna Ganduje ba, har sai da ta cika tattaunawa da masana a wani taronta data gabatar da tsakiyar shekara.

DABO FM ta binciko kungiyar dai tayi nuni da cewa; Shirin da gwamna ya kaddamar na Tilasta Karatun Yara da kuma yinshi kyauta a jihar Kano, yana daga cikin abinda yasa gwamnan ya zama gwarzon kuma mau daraja.

Daga cikin ayyukan da ta lissafo; kungiyar tace Niyyar gwamnan ta gina Kwalegin Ilimi ta yan mata da gwamnan ya kudiri yi, shima abin a yaba ne matuka.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020