Labarai

Kungiyar Kiristoci ta bawa ‘Yan gudun Hijira Naira miliyan 7, buhunhunan shinkafa 500 da kayan sana’a

Kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN, ta kai ziyara sansanin ‘yan gudun hijirar jihar Borno wadanda keda mafaka a Cocin EYN

Kungiyar dai ta ba da gudumuwar kayayyakin abinci da kekunan dinki gasu ‘yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya rabasu da muhallinsu.

‘Yan gudun hijirar da adadinsun yakai 3000 sun samu tagomashi tsabar kudi Naira miliyan 7, buhuhunan Shinkafa guda 500 hadi da kekunan dinki guda 50.

Rev. Dr. Samson Ayokunle, shugaban kungiyar, ya mika wannan gudumuwarna lokacin daya kai ziyara zuwa sansanin yan gudun hijirar.

Shashin Hausa na Muryar Amurka ya rawaito cewa shugaban dai yayi kira ga gwamnati da suma al’umma su kasance masu gaskiya tare da kishin kasa fiye da komai wajen tona asirin tsirarun yan tada kayar bayan.

“Shi ma shugaban cocin EYN da ke unguwar Wulari a Maiduguri, Rev. Bitrus Mahmuda, ya ce mutane da dama suna cikin damuwa saboda wasu an kashe mazajansu wasu kuma ‘ya ‘yan su, sannan ya yi kira da gwamnati da ta kai masu dauki.” -VOA Hausa