Matar Aure ta zabgawa Mijinta Guba a jihar Kano

Karatun minti 1

Daga karamar hukumar Kumbotson jihar Kano, wata matar auren ‘yar shekara 15 ta zubawa mijinta guba a cikin abinci.

Hassana Lawan 15, tayi kokarin kashe mijinta nata Sale Abubakar 35, bayan data zuba masa maganin bera a abincin data kawo masa yaci.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar al’amarin inda tace tini ta cafke matar da ake zargi inda kuma ta aike da mijin zuwa asibiti domin karbar agaji.

“Da misalin karfe 2 na ranar Talata, muka samu labarin wacce ake tuhuma ta zubawa mijinta maganin bera a cikin abinci.”

Ya kara da cewa tini aka garzaya da Sale Abubakar asibitin Murtala dake cikin birnin jihar Kano.

Daga karshe yace zasu cigaba dayin bincike kan matar, kuma da zarar sun kammala zasu mika ta gaban alkali.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog