NNPC: Farashin sauke Man Fetur ya koma N180 – Minista Kachikwu

Karatun minti 1

Karamin ministan Man Fetur na Najeriya, Mr Ibe Kachikwu yace kudin sauke Man Fetur da akeyi yanzu ya zama N180 duk Lita daya.

Ya bayyana cewa kudin sauke man yafi farashin da ake siyar da man a kowanne famfo da karin Naira 35.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Ministan ya bayyana haka ne a jiya Talata a Abuja, babban Birnin Tarayyar Najeriya.

Ministan yace sun dawo da bada tallafin man bayan cire shi da akayi a shekarar 2016 bisa wahala da kuma tashin farashin man a kasuwar duniya.

Da yake magana akan cire tallafi a bana, yace dole sai sunbi abin a hankali saboda idan aka cireshi lokaci daya hakan na jawo cece kuce tare da tafiyar ma’aikata hutun dole saboda zanga-zanga.

“Idan akace meyasa man yake wahala? ana maganar cirewa (Tallafi), tituna zasu cika da masu zanga-zanga, daga haka sai aga an samu kwanaki 5 zuwa 10 ba’a aiki.”

“Muna godewa mutane da suke fahimtar duk abubuwan da mukeyi,

Karin Labarai

Sabbi daga Blog