President Muhammadu Buhari
Labarai

Dole ‘yan Najeriya su dena fita kasashen waje don neman magani -Buhari

Shugaba kasa Muhammadu Buhari yace ‘yan Najeriya su dena fita zuwa kasashen waje domin neman magani.

“Yan Najeriya suna shan matukar wahala wajen fita kasar waje domin neman magani. Wannan ba abu ne mai kyau a wajenmu ba kuma dole ne a dena saboda bazamu iya cigaba da yi ba.”

DABO FM ta tattaro shugaban ya bayyana haka ne yayin taron bude sabbin ayyukan da gwamnatin tayi a asibitin koyarwa na Alex Ekwueme dake garin Abakaliki dake jihar Ebonyi a ranar Juma’a.

Jaridar Punch ta rawaito cewar; Ya bayyana samar da sabbin cibiyoyin domin kula da kuma sa ido wajen faruwar ambali da yashewar kasa a yankin.

Shugaban wanda ya samu wakilcin Ministan Kimiyya da Fasaha, Dakta Ogbonnaya Onu, ya kara da cewa kammala ayyukan zai taimaka wajen samawa mutanen shiyyar da makotansu sauki sakamakon yawaitar samun ambaliya a yankin Kudu maso gabas na Najeriya.

Haka zalika ya bayyana samar da aikin a jihar Ebonyi a matsayin karshen lokacin cin hanci da wani bangare baya samun ayyuka daga gwamnati. Ya kuma bayyana cewa gwamantin bazata bar wasu sassan kasar ba tare da samar da ayyukan ba.

“Mun bawa bangaren lafiya muhimmanci na musamman domin inganta lafiyar al’umma wanda kuma zamu cigaba da yin haka. Ayyukan da muka bude a yau, sun kawo cikas wajen tafiyar da ayyukan wannan asibitin a lokacin da ake gudanar a aikin. Amma yau mun bude su, zamu iya cewa tin daga yanzu, an fara ma’aikata da mutane masu zuwa asibitin sun fara mafana.

“Ina so inyi amfani da wannan dama domin in taya sakataren gwamnati, Mista Boss Mustapha, murna tare da sauran ma’aikatanshi, dan kwangilar da sukayi wannan aiki, Messrs Amayaro Nigeria Limited tare da wadanda suka duba aikin, Messrs Kanode and Associates Limited, bisa jajircewa wajen kammala wannan aikin cikin sauri”

Karin Labarai

Masu Alaka

Zuwan Hanan Buhari daukar hoto Bauchi cikin jirgin saman Shugaban Kasa ya yamutsa hazo

Muhammad Isma’il Makama

Buhari ya bada kyautar magani, gidan sauro, kayyakin gwaje-gwaje da dala 500,000 ga kasar Malawi.

Dabo Online

Buhari ya dakatar da dukkanin Jami’an Gwamnati daga fita kasashen Waje

Dabo Online

To fa: Sanusi ya nemi Osinbajo yayi masa mataimakin shugaban kasa lokacin da Buhari bashi da lafiya

Muhammad Isma’il Makama

Buhari ya dora alhakin hare-haren kisan kiyashi na ‘yan ta’adda a Arewa kan annobar Korona

Muhammad Isma’il Makama

Cikin Hotuna: Ziyarar Shugaba Buhari zuwa birnin Dubai

Dabo Online
UA-131299779-2