Labarai

Kwabid-19: Abdussamad BUA ya bai wa jihar Kano tallafin Naira biliyan 2

Alhaji Abdussamad Rabiu, shugaban kamfanin BUA, ya alkauranta bayar da tallafin biliyan 3.3 ga jihohin Kano da Legas da kwamitin dake yaki da yaki da Kwabid-19 na Najeriya.

Haka zalika ya sanar da baiwa kwamitin yaki da cutar na kasa tallafin tsabar kudi na Naira miliyan 300.

DABO FM ta tattara cewar a ranar 27 ga watan Maris na 2020, shugaban kamfanin ya mika tsabar kudi na Naira biliyan 1 da yayi wa gwamnatin Najeriya akawari a matsayin tallafi.n yaki da cutar Kwabid-19.

Cikin wata sanarwar da Abdussamad ya fitar a yau Lahadi, ya bayyana rashin jin dadi bisa yawan mutuwa da akeyi kwanannan a jihar Kano wadda gwamnati ta kasa yi wa al’umma bayanin dalilin yawan mace-macen.

“Yadda ciwon yake yaduwa abin damuwa ne kwarai musamman a jihohin Kano da Legas duk da kokarin da ake yi wajen yakar cutar. Ina yabawa hukumar NCDC bisa kokarinta a cikin wannan yaki. Sai dai duk da haka ana bukatar kara dagewa.”

Ya bayyana cewar jihar Kano za ta samu tallafin Naira biliyan 2 yayin da jihar Legas za ta samu Naira biliyan 1 a cikin tallafin.

“Duba da abinda yake faruwa yanzu musamman a jihar Kano, cikin hanzari mun yanke bayar da tallafin Naira biliyan 3.3 zuwa ga kwamitin yaki da cutar na NCDC da wasu masu ruwa da tsaki wajen sanya kayan aiki a cibiyoyin gwaji cutar ta jihar Kano da Legas.”

Ya kara da cewa tallafin zai karkata ne wajen sanya kayyakin aiki a cibiyoyin da hukumar NCDC ta kafa a jihohin Kano da Legas.

Karin Labarai

UA-131299779-2