Labarai

Kaduna: Dan majalisar wakilai mai wakiltar Soba ya raba kayan abincin ga al’umma

A kokarin sa na tallafawa al’ummar sa da kayan abinci domin rage masu radadin da ake ciki da kuma na azumin watan Ramadana, Dan majalisar wakilai na kasa mai wakiltar mazabar Soba Hon Ibrahim Hamza, ya bada tallafin hatsi da suka hada da shinkafa da gero da man gyada da magi da dai sauran kayayyakin abinci na yau da kullum.

Da yake kaddamar da bada tallafin ga wakilan al’ummomin da za su amfana da kayan, Dan majalisa Hon Ibrahim Hamza, ya ce duba da halin da kasa da al’umma ke ciki, ya zama ala tilas samar da wannan abinci da ake sa ran dubban al’umma a yankin karamar hukumar Soban za su amfana. Kuma kaya ne da aka kashe kudi sama da miliyan Ashirin wurin siyan su.

Ya kara da cewa, a matsayin sa na dan majalisa, hakkin sa ne ya taimaki duk wani dan asalin karamar hukumar ba tare da la’akari daga wace Jama’iyya ko yanki ya fito ba. Shi yasa ma ya sanya nauo’in al’umma daban-daban da suka hada da ‘yan siyasa da malaman addini da kungiyoyi da kuma ‘yan uwa da abokan arziki da ake sa ran za su amfana da tallafin abincin.

Ya kuma hori wanda za su raba kayan abincin su ji tsoron Allah su yi aiki da gaskiya da kuma adalci ba tare da nunawa wasu ban-banci ba wurin rabon.

Ibrahim Hamza, ya hori al’ummar sa, su cigaba da yiwa kasa da Jihar Kaduna da kuma karamar hukumar Soba addu’a ta musamman domin Allah ya kawo sauki a annobar da ta tsayar da duniya cak yanzu haka.

Da yake maida jawabi a madadin daukacin al’ummar da suka taru a wurin, shugaban Jama’iyyar Apc na karamar hukumar Soba Hon Dayyabu Jumare Kinkiba, Ya gode ma Hon Ibrahim Hamza ne bisa yanda yake aiki ba dare ba rana domin sauke nauyin da yake kansa wurin taimakon al’ummar sa. Kuma shi ma ya ja kunnen wanda za su raba kayan da cewa su ji tsoron Allah wurin aikin na su ba tare da nuna son kai ko kyashi ba.

A jawaban su daban-daban, wasu da suka amfana da tallafin kayan abincin, sun bayyana farin cikin su da abun da Dan majalisa Ibrahim Hamza ya ke masu ba wai a wannan lokacin ba, ko kwanakin baya ya dauki ragamar karishe gine-ginen wasu masallatai a karamar hukumar, kuma suka ce lallai abun a yaba ne.
Sun kuma jinjina masa saboda kaucewa siyasar bangaranci da karamar hukumar Soba ta yi kaurin suna a kai.

Karin Labarai

Masu Alaka

KADUNA: El-Rufa’i ya ruguje dukkanin Jami’an Gwamnatin Kaduna

Dabo Online

Zaben Gwamna: El-Rufa’i na jami’iyyar APC ya lashe zaben gwamnan Kaduna karo na biyu

Kowa na da rawar da zai taka wurin kyautata sha’anin tsaro – Ubangarin Zazzau

Mu’azu A. Albarkawa

Yanzunan: ‘Yan bindiga sun harbe mutum 66 a Kaduna

Dabo Online

Nayi Tir da shigar tsiraicin da Rahama Sadau tayi -Mai Sana’a

Muhammad Isma’il Makama

An fanso dan Majalissar jihar Kaduna awanni kadan bayan anyi garkuwa da shi

Dabo Online
UA-131299779-2