Labarai

‘Babu ranar dawo da cibiyar gwajin Kwabid-19 dake Kano’

Shugaban cibiyar gwajin Koronabairas dake Kano, Nasiru Magaji, ya bayyana cewar babu takamaiman ranar da cibiyar ta jihar Kano za ta dawo aiki.

DABO FM ta tattara cewar tin ranar Laraba aka garkame cibiyar da take kwalli daya a Arewacin Najeriya.

Shugaban yace cibiyar ta bude dakunan gwaje-gwajen cikin cibiyar, sai dai yace basu fara yin gwajin ba, kamar yadda Kano Focus ya rawaito.

“Mun bude dakin gwajin tin jiya (Juma’a), amma ba a fara yin gwaji haka nan kawai bayan bude dakin gwaji. Sai anyi abubuwa da yawa. Su muke yi yanzu.”

Da yake martani kan cewa yaushe za a cigaba da yin gwaji a cibiyar, ya bayyana cewar babu takamaimai lokaci da za a fara gudanar da gwaji a cibiyar.

Karin Labarai

Masu Alaka

Yanzu-yanzu: Mutane 2 sun sake kamuwa da Covid-19 a Kano, jumilla 3

Dangalan Muhammad Aliyu

Yanzu-yanzu: Mutane 10 sun sake kamuwa da Kwabid-19 a Kano, jumilla 37

Dabo Online

Yadda unguwar Fagge a Kano ta zama sabuwar Kasuwar Kanti Kwari da Kofar Wambai

Dabo Online

Yanzu-yanzu: Mutum 2 sun kamu da Koronabairas yau a jihar Kano, jumillar 313

Dabo Online

Ganduje ya sassauta dokar hana fita a Kano

Dabo Online

Tirkashi: Masu dauke da cutar Koronabairas sun yi garkuwa da ma’aikatan lafiya a Kano

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2