Labarai

Kwabid-19: ‘Yan Adaidaita sahu sun ki bai wa Gwamnatin Kano hadin kai

Tun biyo bayan tabbatar da bullar annobar Coronavirus a jihar Kano, gwamnatin Kano ta hana daukar mutane fiye da biyu a babur mai kafa uku, amma direbobin sunyi kunnen kashi inda suke daukan mutane fiye da 2 a cikin baburin nasu.

Dabo FM tayi ido hudu da wani mai baburin nafe dauke da mutane fiye da 2 cikin baburin a kan gadar Kabuga, ranar Talata misalin karfe 7 na dare, wanda wannan ke nuni da masu baburin sunki bin dokar da gwamnatin ta kafa.

Tunda farko dai gwamnatin ta kafa dokar daukar mutum guda a cikin baburin, inda daga baya bayan rokon Allah da Annabi da shugabannin kungiyar suka yi gwamnatin ta kara zuwa mutum 2 domin kare al’umma daga kamuwa da annoba mai sarke numfashi.

Da yake karin bayani, mai magana da yawun hukumar yan sanda, DSP Abdullahi Kiyawa ya bayyana cewa “A ranar farko ta kafa dokar mun cafke baburan Adai-daita sahu fiye da 80 a fadin jihar Kano.”

“Bayan magiya da dai-daito tsakanin hukar yan sanda, gwamnati da shuwagabannin kungiyar babura masu kafa 3, gwamnati ta bada umarnin ayiwa wanda suka karya wannan doka afuwa.”

Inda sukaje suka karbi baburan su a hannun hukumar ‘yan sanda ta hannum shugaban kungiyar direbobin.

Karin Labarai

UA-131299779-2