Zulum ya yaba wa Pantami kan kaddamar da muhimman ayyukan sadarwa 6 a wasu jihohin Najeriya

Karatun minti 1

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya jagoranci wani taro na kaddamar  da wasu ayyuka guda 6 da Ministan Sadarwa, Dr Isa Ali Pantami, ya yi.

An gudanar da taron a hukumar Sadarwa ta Najeriya, wato NCC, a Abuja.

NCC da hukumar Kula da Fasahar Sadarwa ta Kasa, NITDA da kuma Kamfanin Sadarwa na Najeriya ne suka aiwatar da wadannan shirye shirye guda shida da suka shafi inganta hanyoyin sadarwa na ICT a fadin Najeriya.

Da yake jawabi a wajen taron, gwamna Babagana Umara Zulum ya yaba wa Ministan sadarwa Dr Isa Ali Pantami, bisa kokari da yace yana yi da kuma aiwatar da manyan manufofi a ma’aikatar sadarwa ta Najeriya.

“Lamarin tabbatar da wadannan ayyuka guda shida a sassa daban daban na kasar nan ba shakka zai haifar da damai ido dama damar samar da aikin yi da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar nan.

Dr Isa Ali Pantami, ya bada damar hada cibiyar Ilimin kwamfuta a jihar Enugu, Kaduna, cibiyar IT a ABU Zariya.

Haka zalika an samar da cibiyar kula da harkokin kasuwanci IT a cikin garin Kaduna, za kuma a samar da wata a garin Daura ta jihar Katsina da kuma cibiyar harkokin fasaha a jami’ar Legas.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Ministar kudi da tsare tsare ta kasa, Zainab Shamsuna Ahmed, da Minstan ayyuka da gidaje, Raji Fashola.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog