An sake rufe Jami’ar Kaduna da Nuhu Bamalli Polytechnic saboda Korona

Karatun minti 1

Jami’ar Jihar Kaduna da takwaranta ta makarantar kimiyya da ta Nuhu Bamalli da ke Zariya sun sanar da rufe makarantar cikin wani mataki na sake kulle makarantun saboda kara barkewar annobar Korona a Jihar Kaduna.

Tun a karshen makon da ya gabata ne dai ake ta rade-radin sake rufe Jihar ta Kaduna saboda kara samun adadin mutanen da ke kamuwa da cutar.

A sanarwar da jami’in watsa labarai da hulda da Jama’a na makarantar kimiyya ta Nuhu Bamalli da ke Zariya Malam Abdullahi Shehu ya fitar, ya bukaci dalibai su tattara nasu ya nasu su bar harabar makarantar zuwa gobe Talata 15 ga watan Disamba.

A cewar sanarwar, bukatar rufe makarantar ya biyo bayan zaman hukumar gudanarwar makarantar ne a litinin din nan.
Sai dai sanarwar ta nuna babu ranar dawowa makarantar zuwa yanzu, kuma dalibai su cigaba da hutun kirsimeti da na sabuwar shekara.

A bangare guda kuma, Jami’ar Jihar Kaduna ta sanar da rufe makarantar saboda abun da ta kira hauhawar adadin mutanen da ke kamuwa da cutar a kullum rana.

Kuma rufe makarantar zai Fara aiki ne a Laraba 16 ga watan Disamba nan.

Ita ma sanarwar ta bukaci dalibai su cigaba da bin matakan da aka shimfida domin kariya daga cutar Korona.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog