A Gaggauce: Gwamnatin Kaduna ta sake rufe makarantun jihar saboda Korona

Karatun minti 1
Nasiru El-Rufai
Mallam Nasiru El-Rufai. Gwamnan Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta sake rufe makaratun jihar saboda fargabar sake barkewar cutar Korona a jihar.

Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kaduna ce ta  sanar da rufe dukkanin makarantun jihar a cikin wata sanarwa da ma’aikatar da fitar kuma ta aike wa DABO FM mai dauke da sa hannun kwamishinan Ilimin jihae, Shehu Usman Muhammad.

Sanarwa da aka fitar ranar Litinin, ta ce gwamnatin ta dauki matakin ne bisa shawarar ma’aikatan lafiya da hukumomin lafiya na jihar da duniya baki daya.

Kazalika ta ce daga ranar Laraba, 16 ga Disamba, kowacce makaranta a jihar ta rufe.

Ta kuma yi kira ga makarantun jihar da su fito da hanyar da dalibai za su cigaba da karatu a yayin da suke zaune a gidajensu.

DABO FM ta tattara cewar tin kafin sanarwar ma’aikatar, tini Jami’ar Gwamnatin jihar, KASU da Nuhu Bamalli Polytechnic da College of Health Makarfi suka sanar da rufewa saboda fargabar barkewar cutar Korona a karo na biyu.

 

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog