/

Zariya: Dan Majalisa ya horas da matasa sana’o’in dogaro da kai

Karatun minti 1

Matasa maza da mata 2,0310 a karamar hukumar Zaria ne suka amfana da horaswa kan sana’o’i na Dan majalisar tarayya mai wakiltan Zaria Hon. Abbas Tajuddeen.

Da yake magana da manema labarai Jim kadan da kammala horaswan, Babban darkta na Dan majalisar kuma shugaban da ya jagoranci horaswa Injiniya Jamilu Ahmad muhmmad Ya ce, Shirin ya sami nasara duba da yadda mahalarta horaswan ke mai da hankali wajen fahimtar abinda aka koya masu.

Ya kara da cewa, an koya masu yadda ake yin sabulu, manshafawa, turare, Jaka, air frishina, da sauran su. Tare da basu kayan aiki da kuma tallafin dubu goma-goma ga kowanen su domin yaja jari.

Shirin ya sami hadin gwiwa da hukumar dake kula da ‘yan gudun hijira, sune suka baiwa mahalartan kayan aiki, inda Dan majalisar ya baiwa kowanen su dubu goma-goma.

Shuwagabannin Jam’iyyar APC da sauran Al-umma da suka zo wajen horaswan, sun yabawa Dan majalisar, tare da bayyana shi a matsayin zakaran gwajin dafi a Jihar Kaduna.

Kuma sunyi kira ga wadanda suka amfana da horaswan da su dabbaka shi ta hanyar da ya dace tare da yin addu’a da fatan alheri ga Dan majalisar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog