0
An wayi gari da ganin wani abin takaici da fargaba a unguwar Marmara dake cikin gari a jihar Kano, bayan da wasu da ake zargin ɓata-garin matasa ne suka afkawa al’ummar unguwar da sara tare da farfasa motoci da keke nafe dake kwana a gefen kwalta, fiye da motoci 20 ake fargabar abin ya shafa.
Majiyar Dabo FM tayi ido biyu da motoci ciki harda baburin ‘Adaidaita Sahu’, abin ya faru ne a daren Talata, inda mutanen unguwar ke cikin fargaba tare da rashin sanin takamaiman abinda ya haddasa wannan barna.
Har zuwa yanzu dai babu rahoton chafke wadanda suka tafka wannan barna.
