Labarai

Kwamishinan ‘yan sanda ya isa fadar Sarkin Kano domin a fito da shi

Jim kadan bayan tsigewar da gwamnatin jihar Kano tayi wa Sarki Muhammadu Sunusi na 2, rundunar yan sandan jihar Kano ta dunguma zuwa gidan sarkin domin fito dashi daga ciki.

DABO FM ta tattara cewar kwamishinan yan sandan jihar, CP Habu Ali da mukarrabanshi a motoci masu tarin yawa.

Kin tafin zuwan nashi gidan sarkin, jami’an tsaro sun rufe kofar shiga gidan, ‘babu shiga, babu fita’.

Jami’an tsaron sunki yi magana da kowa tare da hana manema labarai shiga domin ganin me yake shirin faruwa.

UA-131299779-2