0
Fitaccen mawakin siyasa a arewacin Najeriya, Dauda Adamu Rarara ya yi ganawar sirri da babban Ministan Sadarwa, Dr Isa Ali Pantami a ofishin ministan dake birnin Abuja a ranar Litinin, DABO FM ta tabbatar.
Kazalika mawakin ya gana da Ministar Kudi, Haj Zainab Ahmad ita ma a ofishinta na birnin Abuja.
“Bayan kammala tattaunawa da Ministan Sadarwa, Dr Isah Ali Pantami da Ministar Kudi, Hajiya Zainab Ahmad a babban birnin tarayyar Abuja”, in ji Rarara.
Sai dai bai bayyana abinda suka tattaunawa ba, ya ce; “Ku saurari sako na gaba.”
