NDDC: Na jinjinawa wa Kwankwaso, Sarki a dumukradiyya – Tsohon Kwamishinan Ganduje

dakikun karantawa

Tsohon kwamishinan aiyuka na jihar Kano, Mu’az Magaji ya jinjinawa tsohon gwamna, Rabiu Musa Kwankwaso wajen kwazon da ya nuna na dankwafar da mukaminsa a hukumar Neja Delta domin almundahanar da tayi wa hukumar katutu.

DABO FM ta rawaito hakan na zuwa ne bayan fallasar da hukumar ta tsinci kanta a ciki na gano wata almundahana da aka yi bayan an zargi hukumar da salwantar da fiye da miliyan dubu 81 cikin wata shida kacal.

Tun da fari majalisa ta aike wa ministan hukumar, Godswill Akpabio, tare da sauran shugabannin hukumar NDDC su bayyana a gabanta domin bincikar yadda wadannan kudade sukai batan dabo.

A Litinin bayan sun bayyana a gaban majalisar, lokacin da yake bada bayanin kashe kudin, shugaban NDDC, Daniel Pondei dai ya tada aljanu a gaban majalisar, inda ake ganin wani salo ne na kaucewa bayyana yanda suka salwantar da kudaden.

Muaz Magaji ya bayyana cewa “A yanzu da ake tsaka da ganin rashin hankalin hukumar NDDC.. Maganar gaskiya ina so na mika jinjinata ga tsohon maigida na RMK domin aje mukaminsa lokacin da ya gano ana wannan almundahanar.”

Bayan yabo ya kara da zaurancen siyasa  “Bahaushe yace yabon Gwani… Sai dai Kash… Gwanin ya zama Sarki a democradiyya…” Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

Tunda fari dai tsohon shugaban kasa, marigayi Umar Musa Yaradua ne ya nada Kwankwaso a matsayin shugaban hukumar mai wakiltar Arewa maso Yamma a 2009, wanda bayan shekara ya aje mukamin cikin Yuni 2010.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog