Kwanaki 122 tin bayan daure IG Wala da kotu tayi akan batun tona cin hanci

Yau Talata, 13 ga watan Agustar shekarar 2019, Ibrahim Garba wanda aka fi sani da IG WALA a cika kwanaki 122 a gidan yari tin bayan daureshi da wata babbar kotu a Abuja ta daureshi.

DABO FM ta tattaro cewa tin dai a watan Afirilun 2019 ne Kotun dake da zama a birnin tarayyar Abuja ta yanke wa IG Wala hukunci daurin shekaru 12 a gidan yari bisa rashin kare kanshi game da zargin cin hanci da yace shugaban hukumar Alhazan Najeriya, Abdullahi Muhammad Mukhtar yake yi.

Tsohon rahotanmu a lokacin da Kotu ta daure IG WALA.

Kotun ta kama IG Wala da laifin batawa shugaban hukumar Alhazai na kasa, Abdullahi Mukhtar suna bisa zarginsa da almundahana da kudin hukumar Naira bilyan 3.

IG Wala dai ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa shugaban hukumar ya yi awon gaba da Naira bilyan 3 na aikin hajjin bara. Ya kuma nuna cewa yana da shaidu.

Kafin zaman Kotun, IG ya rubuta korafi zuwa ga ofishin shugaban Kasa Muhammadu Buhari, hukumar EFFC da ICPC hadi da majalissar Dattijai.

IG ya bayyana cewa wasu shafaffu da mai sun hana shugaba Buhari ganin takardar daya aike.

“An shiga an fita wajen tsayar da hukumar EFFC da ICPC gudanar da bincike akan takardar zargin rashawar daya aike musu.”

Ya kara da cewa majalissar Dattijai ce kadai tayi bincike akan korafin nashi, inda ta bayyana cewa lallai shugaban hukumar Alhazan yayi almundahana tare da batan kudin har biliyan 3.6 a duk shekara.

Yanzu dai alkali ya yankewa IG wala hukunci jimilla har tsawon shakaru 12 a gidan kaso bisa kama shi da laifin fitar da zance batare da hujja ba.

Kotun dai ta kara kama IG Wala da laifin bata suna da kuma rashin gabatar da hujja akan furuci da yayi na batan kudi a hukumar Alhazan.

%d bloggers like this: