Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

#PrayforDadiyata: Kwanaki 10 da bacewar Abu Hanifa Dadiyata ‘Kwankwasiyya’

2 min read

Da safiyar Asabar, a kwanan watan turawa, rahotanni suka tabbar da dauke matashi Abubakar Idris wanda aka fi sani da Dadiyta, a cikin gidanshi dake jihar Kadunan Najeriya.

Abu Hanifa Dadiyata dai ya kasancewa sananne a shafukan sada zumunta musamman shafin ‘Twitter’ inda yayi kwauron suna akan kare muradun darikar Kwankwasiyya da hamma da gwamnatin Ganduje dama APC a kasa baki daya.

Dabo FM ta bincika cewa dai tuni jami’iyyar PDP ta zargi jimi’an tsaro na DSS da kamun Dadiyata, inda shima a nashi bangaren, mai magana da yawun dan takarar gwamanan PDP a jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya tabbatar da zargin da suke yiwa DSS akan kamun Dadiyata.

Sai dai hukumar ta DSS ta bayyana cewa “Babu wani mai suna Dadiyata da yake hannunta.” hasali ma bata tura jami’anta zuwa gidan kowa ba a wannan rana. -Kamar yacce Daily Nigerian ta tabbatar.

DABO FM ta tattaro daga shafin Twitter cewa; Ma’abota amfani da shafin Twitter sun kaddamar da gangami irin na shafin mai taken ‘#PrayforDadiyata’ domin saka matashin a addu’a har Allah ya bayyana shi.

Har yanzu dai akwai masu zargin jami’an na DSS da yin karya akan maganar da suka fada na cewa baya hannunsu.

Shigar da Email domin samun labarai da dumu-dumi

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.