Labarai

Kwanaki 7 da kammala digiri na 2, ya rasu a kan hanyar dawowa Najeriya daga Sudan

Dan Najeriya ya koma ga mahaliccinshi kwanaki 7 da kammala karatun digiri na biyu a kasar Sudan.

Dalibin, Barau Salihu Abubakar, ya kammala karatun digirinshi na 2 a fannin addinin Musulunci (sashin kwarewa akan Qur’ani da kimiyyarshi) a Jami’ar Bakhtalruda dake garin Ed Dueim, mararrabar garin Khartum da Kosti.

DABO FM ta tattara cewar Barau Salihu ya rasu ne akan sakamakon hatsarin mota da ya ritsa dashi a kan hanyarshi da zuwa filin tashi da saukar jiragen kasar ta Sudan domin dawowa Najeriya.

Takardar kammala karatun mamacin wacce DABO FM tayi ido hudu da ita ta tabbatar cewar hukumar Jami’ar Bakhatularda, ta baiwa Salihu Abubakar shaidar kammala karatun a ranar 24 na watan Fabarairun 2020.

An bayyana Mallam Barau Salihu Abubakar, dan asalin jihar Kaduna a matsayin kamilallen mutum, masanin adddinin Islama da iya zamantakewar rayuwa.

DABO FM ta samu sanarwar mutuwar daga wasu makusantan mammacin, sai dai zuwa yanzu mun aike da sakon karta kwana zuwa Jami’ar Bakhatularda da ofishin Jakadancin Najeriya na birnin Khartoum domin ji daga garesu.

UA-131299779-2