Shugabancin darikar Kwankwasiyya ya bayyana shirinsa na hukunta wanda ake zargi da hada bidiyon ‘auren shugaba Buhari’.
Auren da ya bayyana cewa babu batunshi kamar yacce aka tabbatar.
Sunusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun dan takarar gwamnan jihar a PDP, ya bayyanawa Daily Trust cewa kungiyar ta Kwankwasiyya tana gudanar da bincike akan kamun da akayi wa Kabiru Sulaiman, wanda hukumar DSS ta kama.
Sunusi yace da zarar kungiyar ta gama binciken gane matashin a matsayin dan kungiyar ne, zata fito ta fadawa duniya matsayarta akan batun tare da hukunta shi domin ya saba da ka’idoji da manufofin kungiyar ta Kwankwasiyya.
A ranar Asabar ne dai hukumar tsaro ta farin kaya da bayyana kama Kabiru Sulaiman ta hannun kakakinta, Peter Afunanya, a ofishin hukumar dake Abuja.
Hukumar tace tini wanda ake zargi ya amsa lafinsa.
