Labarai

Masu kutsen Iran sun kwace ragamar shafin yanar gizon gwamnatin Amurka

Wasu masu kushe da suka bayyana kansu a matsayin ‘yan kasar Iran, sun kwace ragamar shafin yanar gizo na gwamnatin Amurka a daren ranar Asabar.

DABO FM ta tattaro daga wasu Jaridun duniya da suka hada da The Guardian ta kasar Birtaniya, da Daily Mail duk ta kasar ta Birtaniya.

Hakan na zuwa ne bayan harin da kasar Iran ta kai a wani ofishin Jakadancin Amurka dake kasar Baghdad kwanaki kadan bayan kasar Amurka ta kashe babban kwamandan Sojin Iran.

DABO FM ta tattaro cewa zuwa yanzu dai shafin Fdlp.gov mallakar gwamnatin Amurka ya dena aiki kafin a yanzu da muke hada wannan rahoton, sai dai an dauki hotunan abinda masu kutse a shafin suka wallafa wanda zaku gani a kasa.

Sun rubuta cewar; “Da sunan Allah, mun kwace jan ragamar shafin, daga tawagar cibiyar tsaron kwamfuta na Iran. Wannan kadan ne na daga cikin aikin sanin kwamfutarmu. A shirye muke koda yaushe.”

Karanta labarin a wasu manyan jaridun duniya;

Karin Labarai

UA-131299779-2