Home Kiwon LafiyaGanduje ya bayar da umarnin dinka takunkumin kariya miliyan 1

Ganduje ya bayar da umarnin dinka takunkumin kariya miliyan 1

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umarnin dinka tukunkumin rufe hanci har guda miliyan 1 wanda a cewarshi zai karfafa matakan kare yaduwar annobar Koronabairas a jihar Kano.

Da yake ganawa da manema labarai akan batun, Ganduje yace gwamnatin za ta kafa dokar da zata tilastawa al’umma sanya kyallayen a fuskokinsu a harkokinsu na yau da kullin da zarar an kammala dinka su.

Sai dai DABO FM ta tattara cewar al’ummar dake rayuwa a jihar Kano sun haura mutane miliyan 12.

A jawabin shugaba Muhammadu Buhari jiya Litinin, ya bayyana sanya dokar zaman gida na tsawon makonni biyu a jihar duk a shirin da yace gwamnati tana yi domin dakile cutar a Najeriya baki daya.

Haka zalika shugaban hukumar NCDC ya bayyana cewar cibiya daya tilo ta gwajin cutar Kwabid-19 a aka rufe ta jihar Kano, za ta cigaba da aikinta daga gobe.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00