Kiwon Lafiya

Likitoci guda 10 a Kano sun kamu da cutar Kwabid-19

Likitoci 10 a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano sun kamu da cutar Kwabid-19.

Likitocin sun kamu ne yayin da da suke duba marasa lafiya a cikin asibitin, kamar yadda shugaban kungiyar Likitoci reshen asibitin, Dr Abubakar Nagoma ya tabbatarwa da Kano Focus.

Shugaban ya bayyana cewar zuwa yanzu an killace 8 daga ciki a cibiyoyin da aka ware wa masu dauke da ciwon, 2 daga ciki suna gidajensu sun killace kansu.

“Duk mun bi duddugin wadanda sukayi mu’amala da su. 8 daga cikinsu suna cibiyoyin killace masu cutar, 2 daga cikinsu suna gida sun killace kansu sakamakon rashin nuna alamun cutar.”

Ya bayyana cewar an yi wa likitocin da wasu ma’aikatan asibitin da dama gwajin cutar wanda a yanzu haka ake jiran sakamakonsu da adadinsu ya kai kusan 100.

“Mu na jiran sakamakonsu cikin mako 1 domin mu san makomar ma’aikatan asibitin.”

Shugaban ya daura alhakin kamuwar likitoci bisa rashin sanya takumkumi fuska da marasa lafiyar da suke zuwa asibitin ba sa sanyawa da kuma rashin isassun kayyakin kariya da likitocin ke sanya wa.

Ya bayyana cewa akwai babban kalubale kan yadda wasu marasa lafiya suke boye bayanai da yake nuna suna dauke da cutar ta Kwabid-19 wanda a cewarshi hakan barazana ne ga likitoci da sauran ma’aikatan lafiya.

Haka zalika yace sun yi barazana daina duba marasa lafiya a asibitin idan har asibitin bai sama musu kayyakin da zasu kare kansu ba, duk da a cewarshi asibitin sun ce gwamnatin tarraya ce ba ta aike musu da kayayyakin kariyar ba.

Adadin masu dauke da cutar Kwabid-19 dai a Najeriya ya na matukar karuwa musamman a arewacin Najeriya.

Zuwa yanzu da safiyar yau Talata 5 ga Mayu, mutane 2802 ne suka kamu da cutar ta Kwabid-19 inda mutane 365 suke a jihar Kano tare da samun mutuwar mutane 8 a jihar.

Karin Labarai

Masu Alaka

Yanzu-yanzu: Mutum 2 sun kamu da Koronabairas yau a jihar Kano, jumillar 313

Dabo Online

Tirkashi: Masu dauke da cutar Koronabairas sun yi garkuwa da ma’aikatan lafiya a Kano

Muhammad Isma’il Makama

Duk da dokar hana fita, an gudanar da Sallar Juma’a a Kano

Dangalan Muhammad Aliyu

Yanzu-yanzu: Mutane 29 sun sake kamuwa da Koronabairas a Kano, jumillar 342

Dabo Online

Kwabid19: Zamu gwada daukacin Almajiran Kano – Ganduje

Dabo Online

Yanzu-yanzu: An kara tsawaita dokar kulle a Kano na tsawon sati 2

Dabo Online
UA-131299779-2