Copyrighted.com Registered & Protected

Limami ya bayyana shirin bude masallacin ‘yan luwadi a Australia

Nur Warsame ya bayyanawa duniya matsayinshi na kasancewa dan luwadi a shekarar 2010.

Limamin dan asalin kasar Somalia ya yanke shawarar bude masallacin daya kira gidan duk wani dan luwadi ko ‘yar madigo da dake jin kunyar bayyanawa duniya matsayinsu.

Warsame yanzu haka yana aiki tare da wasu manyan inginiyoyi da mazana na kasar ta Australia, domin ganin ya cimma burinshi, na bada mafaka ga wadanda danginsu suka kora saboda kasancewarsu ‘yan madugo ko luwadi.

Mutanen alkaryar Melbourne sunce Wursame yada aure kuma mahaddacin Al-qur’ani ne, sun bayyana rashin jin dadinsu da yacce ‘yan uwanshi musulmai suka koreshi, suka kuma fitar dashi daga cikin danginsu.

Ana sa ran bude masallacin a acikin wannan shekarar, ina nan muna aiki da manyan Inginiyoyi da manyan ‘yan kwangila domin ganin an gaggauta bude wannan masallacin. Bude wannan masallaci zai bawa matasa kariya, tare da tabbatar da an basu kulawa da shawarwari domin kauracewa masu yi musu barazanar  dukan halaka.

Malamin yace “Kafin in gane ni dan luwadi ne, inada aure kuma muna zaune da matata lafiya, amma yanzu naga cewa bazan iya yin rayuwa guda biyu ba shiyasa na karkata kan wannan layi.

%d bloggers like this: