//

Waiwaye: Lokacin da Iran tayi maraba da hukuncin rataye Saddam Hussain

dakikun karantawa

Har yanzu ana cigaba da nuna damuwa da kisan jagoran tsaron kasar Iran, Qassim Sulaimani, da kasar Iran da dukkanin mabiya akidar Shi’a suke yi a fadin duniya. A wani bangaren wasu suke nuna rashin damuwarsu ga kisan Qassim musamman kasashen yamma da wasu a’umma musulmi.

Masana tarihi suna ganin cewar magoya bayan tsohon shugaban kasar Iraqi, Saddam Hussain, da wasu musulman da suke ganin tsaurin hukuncin kisan Saddam, zasuyi murna da kisan Janaral Qassim Sulaimani bisa da irin alakar rashin jituwa dake tsakaninsu da Iran.

DABO FM tayi waiwaye zuwa shekarar 2006, lokacin da kasar Iran tayi maraba da hukuncin rataya da kotun kasar Iraqi tayi wa Saddam Hussain.

Iran ta hannun mai magana da yawun ma’aikar harkokin kasar wajen Iran a wancen lokaci, Mohammad Ali Hussain, ya bayyana yacce kasar Iran ta karbi hukuncin kisan Saddam da hannu bibbiyu.

Gidan Talabijin na BBC dake kasar Birtaniya, ya rawaici kalaman da ma’aikatar harkokin wajen Iran tayi a ranar Lahadi 5 ga watan Numbar shekarar 2006 da karfe 10:36 na dare a agogon Najeriya da Nijar.

“Jamhuriyar Musulunci ta Iran, na maraba da hukuncin kisan da aka yanke.”

“Ko da Saddam da mutanenshi suka yi wadannan laifuka, bazamu taba mantawa da mutanen yamma wadanda suke bashi kariya, wanda suna goyon bayanshi kuma sukayi masa bita da kulli na shirya yake masa hukuncin laifukan da ya aikata.” – Cewar Mohammad Ali Hussain

Haka zalika, a gwamantin kasar Iran, ta hannun mai magana da yawunta, Gholam Hossein Elham, ta bayyana Saddam Hussain a matsayin “mai mulkin karfi da yaji kuma mai babban laifi, tare da yin kira da a tabbatar da rataye Saddam.

Tushe: BBC, TEHRAN NEWS, RADIO LIBERTY EUROPE.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog