Rudunar sojin ta samu nasarar kashe yan bindiga dadi sama da guda ashirin.
Rundunar sojojin na shashin Operation Sharar Daji, ta dakile wani harin da wasu yan ta’adda suka kai a biranen Zamfara da Katsina.
Rundunar tace ta kashe ‘yan ta’addar 21, ta kama 7 tare da kwato wadanda ‘yan ta’addar sukayi garkuwa dasu wanda adadinsu ya kai 89 duk a sumamen da sukayi a jihar Zamfara da Katsina daga 22 ga watan Janairu zuwa 28 ga watan na shekarar 2019.
Mukaddashin jami’an yada labarai na Rundunar Operation sharan Daji, Mayor Clement Abiade a cikin wata sanarwa yace “An sace mutuna shida a kauyen Asowa dake karamar hukumar Bafe da Birnin Magaji.
Abiade ya kara da cewa sun kwato bindiga guda daya, bindigogi kirar hannu, tabar wiwi da sauran kwayoyi masu saka maye.
