//
Wednesday, April 1

Yakin Duniya III: Majaisar Iraqi ta yanke hukuncin fatattakar sojojin Amurka daga kasarta

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Majalisar Dokokin Kasar Iraki ta yi wani zama na musanman inda ta yanke hukunci akan fitar da sojojin Amurka daga kasarta.

Rahoton Dabo FM ya bayyana Majalisar dai karkashin shugabancin Muhammed al -Halbusi ta yi zaman ne domin tattaunawa akan yadda sojojin Amurka ke kasar nata.

‘Yan majalisu ‘yan Shi’a sun dinga rera taken A’a ga Amurka, ‘Yanci ga Baghdad, A kori Amurka daga Iraki gabanin zaman. Kamar yadda jaridar TRT ta rawaito.

A zaman da ya samu halartar firaministan Iraki Adil Abdulmehdi an duba lamarin kasancewar sojojin Amurka a Irakin.

Daga karshe dai majalisar ta yanke hukuncin fitar da sojojin Amurkan daga kasar Iraki.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020