Majalissar Dattawa ta bankado wata badakala ta Naira tiriliyan 3 a ma’aikatun gwamnati

Karatun minti 1

Majalissar dattawan Najeriya ta bankado yadda wasu hukumomin Najeriya su ka yi dabdalar tsabar kudaden da adadinsu ya kai Naira tiriliyan 3.

Kwamitin kudi majalissar karkashin jagorancin Soloman Adeola ya ce hukumomin gwamnatin sama da guda 60 ne suka tafka badakalar. Hukumomin masu samar da kudaden shiga da ya kamata a sanya su a lalitar gwamnati, sun kasa biyan kudaden cikin asusun hada-hadar kudade na CFR.

Shugaban ya ce rashin shigar da kudaden ya taimaka wajen tabarbarewar kudin gwamnati wanda ya sanya gwamnatin ta ke cin bashi musamman daga shekerar 2014.

Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, ya yi wa sahin Hausa na Muryar Amurka haske kan binciken, ya ce hukumomin sun take doka wajen kashe kudade ba tare da neman izini daga zauren majalissar ba.

Ya ce dole ne hukumomin su mayar da kudaden, in kuma ba haka ba a hana gwamnati basu kudaden tin da su ma su na iya samar wa kansu kudade. Ya ce yin hakan zai rage wa gwamnati yawan kashe kudade.

Kwamitin kula da harkokin kudi na majalisar dattawan ya ce dole hukumomin gwamnatin nan 60 su mayar da wadanan makudan kudade, domin rashin zuba su a lalitar gwamnati ya sabawa tanadin kudin tsarin mulki da dokar kula da kasafin kudi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog